Rashin Jami’ar Mallakin jihar a shiyyar Kano ta Arewa na kokarin bayar da yankin baya – Alh. Mustapha Ahmad Gwadabe

Date:

Daga Shehu Hussaini Ahmad Getso

An bukaci Gwamnatin jihar Kano data duba yuwuwar samar da karin Jami’i mallakin jihar a shiyyar Kano ta Arewa.

Wani dan gwagwarmayar kawo cigaba a jihar Kano Alh Mustapha Ahmad Gwadabe Gwarzo ne ya bukaci hakan a zantawarsa da wakilin Kadaura24 a Kano.

InShot 20250309 102512486
Talla

Alh Mustapha Gwadabe Gwarzo ya ce baya ga yadda a lokaci irin wannan ake tsananin bukatar karin jami’o’i a jihar Kano, akwai abubuwa biyu da suka dace su zama ababen kallo a wajen mahukunta.

Na farko Jami’o’i guda biyu mallakin jihar Kano da ake da su a halin yanzu, daya tana shiyyar Kano ta kudu wato Aliko Dangote University of Science and Technology Wudil, yayin da dayar ta ke a shiyyar Kano ta tsakiya wato North West university, Wanda hakan ke nuni da cewar shiyyar Kano ta Arewa anso a barta a baya.

Yan uwan wata mata sun zargi Asibitin Malam Aminu Kano da sakaci wajen mutuwar yar uwarsu

Na biyu ya ce cikin kananan hukumomi goma sha uku na Kano ta Arewa babu inda ya fi da cewa da gina sabuwar jami’a a halin yanzu fiye da karamar hukumar Gwarzo,domin ko dai cikin kafatanin tsofaffin kananan hukumomin da aka san tsohuwar jihar kano dasu(Kano/Jigawa), karamar hukumar ta Gwarzo ce kadai a yanzu haka bata da wata babbar makaranta ta kashin kanta, banda reshe na wadansu manyan makaranta, Adon haka itace karamar hukumar da ta fi a yi sabuwar jami’a mallakin jihar kano a halin yanzu.

Da yake magana kan gudunmuwar da karamar hukumar za ta iya bayarwa wajen tabbatuwar wannan al’amari, Alh. Mustapha Gwadabe Gwarzo ya ce karamar hukumace da Allah ya bata manya manyan malaman ilimi da daliban ilimi da za su iya zama malamai, ma’aikata ko dalibai.

A saboda haka dai sai ya bukaci Gwamnatin jihar Kano da duk wani mai ruwa da tsaki da su duba wannan fafutuka da su ke da idon basira don cigaban al’ummar jihar Kano baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Tinubu ya Iso Kano domin ta’aziyyar Dantata

Shugaban Nigeria Bola Ahmad Tinubu ya iso jihar Kano...

ALGON ta Kano Sa’adatu Soja ta sami sabon matsayi a kungiyar ALGON ta Ƙasa

Daga: Aliyu Danbala Gwarzo. Shugabar karamar hukumar Tudunwada kuma ALGON...

Da dumi-dumi: Tinubu zai zo Kano

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu zai zo Kano ranar...

Tinubu ya sauya sunan jami’ar Maiduguri zuwa Sunan Muhd Buhari

Shugaba Bola Tinubu ya sauya sunan Jami'ar Maiduguri zuwa...