Hukumar almajirai da yaran da ba sa zuwa Makaranta ta kaddamar da yi wa yaran da ba sa zuwa Makaranta Rijista a Kano

Date:

Daga Saminu Ibrahim Magashi

 

Hukumar kula da almajirai da yaran da ba sa zuwa Makarantar ta gwamnatin tarayya ta yi gangamin kaddamar da yi wa yaran da ba sa zuwa Makaranta su  kimanin 200 rijista a kano.

Da yake jawabi a yayin taron shugaban hukumar na kasa Dr. Muhammad Idris ya bayyana cewa sun ɗauki matakin yiwa yaran rijista ne domin Sanin hakikanin yawansu don tallafawa rayuwarsu da ingantata ta hanyar mayar da su Makaranta.

InShot 20250309 102512486
Talla

“Wannnan ya na daga kudirin gwamnatin tarayya mai ci na tabbatar da cewa kowanne yaro da ya Sami ilimin da ya dace, don haka ta lashi takobin mayar da yaran da ba sa zuwa Makaranta zuwa Makarantar”. Inji Dr Muhammad Idris

Ya ce wannan ne karon farko da aka kaddamar da fara yi wa yaran rijista, kuma ya ce za su tabbatar da cewa sun cikawa shugaban kasa muradinsa na koyar da ya’yan al’umma kyauta tare da daukar nauyin malaman da za su rinka koyar da su.

Gwamnan Kano ya yi sabbin nade-nade

“Za mu koyawa yaran harsunan larabci da turanci domin tabbar da cewa su ma sun sami gogayya tsakaninsu da sauran ya’yan al’umma”.

IMG 20250415 WA0003
Talla

A jawabinsa wakilin Yamma malam Aminu Tijjani Sunusi ya bayyana matukar farin cikinsa tare da rokon wannan hukuma da ta rubanya wannna kokarin na ta acikin qaramar hukumar gwale tayanda kowacce mazaba zata rabauta da wannna tsari.

Gangamin yin rigistar ya gudana ne a filin unguwar galadanci dake karamar hukumar Gwale ya kuma samu halartar muhimman mutane ciki har da masu unguwannin yanki, iyayen Yara da dai sauransu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rasuwar Buhari: Majalisar Nigeria ta dakatar da duk aiyukanta

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Majalisar dokokin Nigeria ta dage zamanta...

Gwamnati ta baiwa ma’aikata hutu saboda rasuwar Muhammad Buhari

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gwamnatin jihar Katsina karkashin gwamna Umar...

Bayan tura Kashim ya taho da gawar Buhari, Tinubu ya ba da umarnin sassauta Tutar Nigeria

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bada umarnin ayi kasa...

Yanzu:yanzu: Tsohon shugaban Nigeria Buhari ya rasu

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un!!! Allah yayi wa tsohon shugaban...