Daga Rahama Umar Kwaru
Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya amince da kashe Naira miliyan 200 domin sayo ababen hawa don bayar da su bashi ga malaman makarantun firamare da sakandare a fadin jihar,
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa Kadaura24, ya ce za a samar da ababen hawan ga malaman ne a wani mataki na inganta jin dadin ma’aikata da kuma zaburar da ma’aikatan koyarwa.

An tsara tsarin ba da bashin ne don taimaka wa malamai don su mallakin ababen hawa cikin sauki da kuma sauƙaƙa musu ƙalubalen sufuri da suke fuskanta.
Gwamna Yusuf ya bayyana hakan ne a lokacin bikin kaddamar da rabon kayan koyarwa ga makarantun gwamnati, a wani bangare na sake fasalin ilimi na gwamnatin sa.
Za mu yi aikin hanyar Utai zuwa Kademi – Shugaban karamar hukumar Wudil
“Mun fahimci rawar da malamai ke takawa wajen inganta makomar ‘ya’yanmu, wannan shirin bayar da lamuni na daya daga cikin manyan dabarunmu na tallafa wa jin dadin su da kuma bunkasa aikin koyarwa a jihar Kano,” inji gwamnan.
Gwamna Yusuf ya jaddada kudirinsa na inganta samar da ababen more rayuwa musamman a bangaren da ya shafi ilimi, inda ya bayyana malamai a matsayin ginshikin ci gaban kowacce al’umma.