Daga Aliyu Danbala Gwarzo
Tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo, da Tsoffin Mataimakan Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, Namadi Sambo da Tsoffin Shugabannin Majalisar Dattawa, Ken Nnamani, Paius Ayim sun isa wurin taron kaddamar da littafin tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido.
Kadaura24 ta rawaito tsohon shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Iyorchia Ayu, shi ake sa ran zai duba littafin tarihin rayuwar Lamido mai suna “Being True to Myself”.

Daga cikin wadanda suka halarci taron kaddamar da littafin da ake gudanarwa a cibiyar taro ta NAF da ke Abuja, akwai dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour a 2023, Peter Obi, sannan gwamnonin Gombe, Muhammadu Yahaya; Jigawa, Umar Namadi; da Plateau, Caleb Mutfwang.
Haka kuma akwai manyan mutane da suka halarci taron, wadanda suka hada da tsohon Gwamna Gabriel Suswam (Benue), Ahmed Makarfi (Kaduna), da Babangida Aliyu (Niger), (Cross Rivers), Liyel Imoke da dai sauransu.
Cikakken bayani na nan tafe