Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Shugaban karamar hukumar Wudil Abba Muhammad Tukur ya sha alwashin yin aikin hanyar da ta tashi daga garin Utai na karamar hukumar Wudil zuwa garin Kademi na karamar hukumar Gaya.
Kadaura24 ta rawaito wani Kabiru Isa Tata Kademi ne ya roki shugaban karamar hukumar da ya yi wa Allah da Manzonsa ya yi musu aikin hanyar data tashi daga Utai zuwa kashe a sashin mayar da martani (Comment section) na shafin Facebook na Arewa Radio.

Nan take kuma shugaban karamar hukumar ta Wudil Abba Muhammad Tukur ya mayar masa da martani cikin lafuza masu dadi.
“Insha Allah za mu duba yiwuwar yinta (hanyar Utai zuwa Kademi) Ka san aikin ya hada kananan hukumomin guda biyu (Wudil da Gaya)”. Inji shugaban karamar hukumar Wudil
Ku cusawa mutane kishin jihar Kano don ba mu da jihar da ta fita – Waiya ga Limamai
Wannan ta sa kadaura24 ta tuntubi Babban mai taimakawa shugaban karamar hukumar kan harkokin yada labarai Abba Ashiru, inda ya ba mu tabbacin tunda shugaban ya yi wancan alwashin to babu shakka zai aikin nan ba da jimawa ba.
” Ai tunda Abba Muhammad Tukur har ya yi masa martani ko ya ba shi amsa nan take nasan nan ba da jimawa ba, za a fara aikin saboda muhimmancin da hanyar ke da ita”. Inji Abba Ashiru
Tabbas mutane da yawa suna amfana da aikin kuma idan aka yi aikin zai saukakawa al’ummar kananan hukumomin wudil da Gaya. Kai wai dai nasan aikin zai zama na hadin gwiwa ne tsakanin Wudil da Gaya kuma da zarar komai ya daidaita za’a fara aikin hanyar.