Hajjin bana: Za mu yi duk abun da ya dace don kyautata walwalar alhazan Jihar Kebbi – Amirul Hajji

Date:

Daga Ibrahim Sidi Muhammad Jega.

 

Shugaban kwamitin aikin hajin bana a jihar Kebbi, wato Amirul Hajji, mai martaba Sarkin Kabin Argungu, Alhaji Dr. Samaila Muhammad Mera (CON), ya bukaci masu ruwa da tsaki a aikin hajjin bana da su baiwa kwamitinsa hadin kai don gudanar da Ibadar cikin nasara.

” Wannan babban aiki ne Gwannan Kebbi ya dora mana, don haka akwai bukatar kowa ya yi iya kokarinsa don mu sauke wannan nauyi da aka dora mana, ta hanyar samar da walwala ga alhazan jihar Kebbi”. Inji Sarkin Kabin Argungun.

IMG 20250415 WA0003
Talla

Alhaji Samaila Mera ya bukaci hakan ne yayin zaman farko da kwamitin ya yi da hukumar Jin dadin Alhazzai ta jihar a karkashin Jagorancin Shugaban Hukumar, Alhaji Faruku Aliyu Enabo (Jagaban Gwandu).

Ya godewa gwannan jihar Kano Kwamared Nasiru Idris (kauran gwandu), tare da baiwa gwamnan tabbacin da shi da yan tawagarsa za su yi aiki tukuru don ganin ba a sami wata matsala ba tun daga nan gida Nigeria har zuwa kasa mai tsarki.

Da dumi-dumi: Sarki Aminu ya nada sabon Galadiman Kano

Da ya ke jawabin maraba, Shugaban Hukumar Jin dadin Alhazzai, Alhaji Faruku Aliyu Enabo Jagaban Gwandu, ya yi godiya da Gwamnan jihar Kebbi, a bisa cikakkiyar kulawa da ya ke baiwa hukumar, da kuma gabatar da kwamitin aikin hajjin bana cikin lokacin da ya kamata.

InShot 20250309 102403344

Jagaban Gwandu, ya bayyana cewa Hukumar zata ba da cikakken goyon baya ga kwamitin domin samun nasarar aikin Hajjin na bana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...

Majalisu na neman sauya lokacin zabuka a Nigeria

Majalisar Dokoki Ta Ƙasa Ta Gabatar Da Kudirin Sauya...

Kungiyar Lauyoyi yan asalin jihar Kano sun mika korafi ga kasashen Amuruka Ingila da UN kan zargin kisan a Tudun Wada

Kungiyar Lauyoyin Yan Asalin Jihar Kano (National Forum of...

Da dumi-dumi: ASUU ta sanar da ranar da zata fara yajin aiki

Shugabancin Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta umurci...