Daga Aliyu Danbala Gwarzo
Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya taya Abubakar Abdulkadir Dangambo murnar zama shugaban sabuwar kungiyar mawallafa labarai a yanar gizo ta jihar Kano dake karkashin kungiyar yan jaridu ta kasa (NUJ) .
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa Kadaura24 a ranar Litinin.

Gwamna Yusuf ya bayyana zabar Dangambo a matsayin wani mataki na cigaba a fagen yada labarai na zamani.
Ya kuma yabawa shugabannin kungiyar NUJ Kano a karkashin jagorancin Kwamared Sulieman Dederi bisa nasarar kafa sabuwar kungiyar ta mawallafa labarai a yanar gizo, wanda a cewarsa hakan zai kara kaimi ga kokarin da kafafen yada labarai na gargajiya suke yi wajen inganta gaskiya da gaskiya da rikon amana.
Hukumar Shari’a ta Kano ta Gargadi Alkalai 2, ta kuma dakatar da Magatakarda 2
Gwamnan ya bayyana cewa ya na da kwarin guiwar cewa a karkashin jagorancin Dangambo, kungiyar za ta sami gagarumin ci gaba a jihar Kano da ma sauran kasashen duniya.
Ya ba da tabbacin gwamnatinsa za ta baiwa kungiyar goyon bayan da hadin kan da ake bukata domin inganta aiyukan ya’yan kungiyar.
Gwamna Yusuf ya yi wa Kwamared Dangambo da sauran Shugabannin fatan samun nasara da kuma tasiri, inda ya bukace su da su yi aiki tukuru wajen bunkasa kungiyar da inganta aikin jarida.