Bayan dawo da Gwadabe Anti daba, Yansanda sun kama yan daba 33 a Kano

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Rundunar Yansanda ta Kasa reshen jihar Kano ta ce ta kama yan daba 33 da ake zargi da ta da hankalin al’umma da fashi da makami da hada-hadar muggwan kwayoyi.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na Rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya aikowa Kadaura24.

IMG 20250415 WA0003
Talla

Sanarwar ta ce runduna karkashin jagorancin O/C Anti daba CSP Bashir Musa Gwadabe ne ya jagoranci aikin wanda aka yi shi daga ranar 23 ga Wannan watan na Afirilu zuwa 28 ga watan.

Ya ce an gudanar da aikin ne a kwaryar birnin Kano, bayan samun bayanan sirri inda aka kama wadanda ake zargin da muggan makamai da kwayoyi da saura makaman da ake amfani da wasu wajen yiwa mutane fashi da makami.

Sabon Rikici ya Barke a Jam’iyyar NNPP ta Karamar Hukumar Dawakin Tofa

Kiyawa ya ce kamar yadda Babban Sufeton yansanda na kasa IGP Kayode Adeolu Egbetokun, ya ba da umarnin samar da zaman lafiya a Kasa, rundunar yansanda ta jihar Kano ta himmatu wajen ganin ta samar da zaman lafiya a a jihar Kano.

InShot 20250309 102403344

Kwamishinan yansanda na Kano CP Ibrahim Adamu Bakori ya yabawa al’ummar jihar Kano bisa yadda suke baiwa rundunar hadin Kai da goyon baya don ganin an sami zaman lafiya a Kano.

Za a iya sanar da Rundunar duk wani abu da ba a yarda da shi ba ta wadannan lambobin :
– 08032419754
– 08123821575
– 09029292926.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta dakatar da nuna tallan maganin Gargajiya a Fina-finai da yawo a tituna

A wani mataki na tabbatar da bin ka'idoji tare...

Da dumi-dumi: NNPP ta nemi afuwar Tinubu kan kalaman suka da ake zargin Kwankwaso ya yi masa

  Jam’iyyar NNPP ta nemi afuwar Shugaban kasa Bola Tinubu...

Gwamnatin Kano ta dakatar da Dadin kowa, Labarina, Jamilun jidda da wasu fina-finai 19

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   A kokarinta na tabbatar da ana...

2027: Hon Abdulmumin Jibrin Kofa ya bayyana Matsayarsa kan takarar gwamnan Kano

Daga Zakariya Adam Jigirya   Dan Majalisar tarayya mai wakiltar kananan...