Rundunar yan Sanda a Kano ta yi Nasarar Kama Aljan Mai Satar adaidaita sahu

Date:

Daga Jidda Abubakar Diso
Yayin da wasu matasa ke cigaba da aikata laifuka, rundunar yan sandan jihar Kano ta baza komarta domin cafkewa tare da hukunta masu aikata laifi, wanda a ranar 24 ga watan da muke ciki ta samu nasarar cafke wanda ake zargi da fashi da ta dade tana nemansa ruwa a jallo Mai Suna Sabitu Ibrahim, wanda aka fi sani da Aljan, dan kimanin shekaru 18 daga garin Kaburma Yan Daddawa, cikin karamar hukumar Dawakin Tofa ta jihar Kano.
Rundunar tace ta kama aljan din aka wani babur mai kafa uku, mai lamba GRR77QA da kuma lambar KAROTA KMC 1106.
Sanarwa da kakakin Rundunar Yan Sanda ta kasa reshen Jihar Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar tace an kama Aljan ne sakamakon yunkurin kwace wani babur mai kafa uku (Adaidaita Sahu) da yayi a hannun matukinsa a unguwar Dorayi, wanda yayi amfani da wayar Kebur ya shake wuyan mai babur din, dakyar ya kwace ya gudu da mummunan rauni a wuyansa, hakan ya baiwa Aljan damar tafiya da babur din.
 Sai dai kuma bayan faruwar lamarin, rundunar yan sanda karkashin “Operation Puff-Adder karkashin jagorancin SP Buba Yusuf, suka fara gudanar da bincike, kuma cikin binciken ne suka kamo wasu matasa guda biyu, Abdullahi Sulaiman mai shekaru 28 daga unguwar Gwale da kuma Abubakar Muhd mai shekaru 21 daga unguwar Hausawa duk a birnin Kano, bisa zarginsu da siyan wasu sassa na babur din da Aljan ya kwace, da kuma wani babur mai lamba FGE212QX, sai kuma lambar KAROTA 4636 KMC, da aka same su a tare dasu.
Sanarwar da Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar a daren jiya, ya tabbatar da kama wasu rukunin matasa da ake zargi da satar wasu babur mai kafa biyu guda biyar, Muhd Saidu dan shekara 31 daga unguwar Gobirawa Yan Yashi da kuma Abdullahi Tahir mai shekara 35 daga unguwar Kofar Ruwa, dukkansu a birnin Kano, wanda kakakin ya bada lamar waya 08105359575 domin tuntubar hukumar ga wadanda aka sace musu wadannan babur, ko kuma su tuntubi kakakin kai tsaye.
Kwamishinan Yan Sandan Jihar Kano CP Sama’ila Shu’aibu Dikko, ya godewa al’ummar jihar Kano baki daya bisa gudummawa ta addu’a, kwarin gwiwa da kuma goyon baya da suke basu, ya bukaci a cigaba da basu hadin kai wajen gudanar da ayyukansu, musamman addu’a da kuma kai rahoto ga ofishin yan sanda mafi kusa idan aka lura da wani abu da ba’a yarda dashi ba, ba tare da daukar doka a hannu ba, ko kuma a kira su a wadannan lambobin waya, 08032419754, 08105359575, 08076091271, ko akan manjahar “NFP Rescue Me” wanda za’a iya dakko shi akan Play Store.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bayan shekaru 20, Kotun Ƙoli ta sanya ranar yanke hukunci kan rikicin masarautar Gwandu

Kotun Koli ta sanya ranar yanke hukunci kan daukaka...

Hukumar Shari’ah ta kaddamar da kwamatoci domin kawo sauye-sauye game da cigaban Shari’a a jihar Kano

  Hukumar Shari'ah ta jihar Kano karkashin jagorancin mukaddashin shugabanta...

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...