Daga Maryam Muhammad Ibrahim
Kwamitin majalisar wakilan Nigeria mai kula da gyaran kundin tsarin mulkin kasar ya gabatar da wasu karin Jihohi 31 a yayin zamansa na wannan rana ta alhamis.
Idan har ta tabbata zai zama an sami Jihohi 67 a Nigeria.
Sabbin Jihohin da ake son karawa su ne Okun, Okura da Confluence states daga jihar Kogi; Benue Ala da Apa daga jihar Benue; FCT state; Amana state daga jihar Adamawa; Katagum daga Bauchi, sai Savannah state daga Borno da kuma jihar Muri daga jihar Taraba.
Sauran su ne New Kaduna da Gujarat daga jihar Kaduna; Sai Tiga da Ari daga jihar Kano, Kainji daga Kebbi; Etiti da Orashi karin kan Jihohi da ake da su a kudu maso gabas, sai Adada daga Enugu, Orlu da Aba daga shiyyar kudu maso gabas .
Iftila’i: Almajirai 17 sun kone kurmus 15, sun jikkata sanadiyya wata gobara
Ragowar su ne Ogoja daga Cross River, Warri daga Delta, Ori da Obolo daga jihar Rivers; sai Torumbe daga Ondo; Ibadan daga Oyo, sai kuma Lagoon daga Lagos, Ogun, Ijebu daga jihar Ogun da kuma Oke Ogun/Ijesha daga Jihohin Oyo/Ogun/Osun .