Mai Martaba Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero yayi wata ganawa ta sirri da Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu mintina kadan kafun tashinsa zuwa kasar Faransa.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran Sarkin Abubakar Balarabe kofar Na’isa ya sanyawa hannu kuma ya aikowa Kadaura24.
Ganawar da Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi da shugaban kasar tana da nasaba ne da iftila’in daya faru ga al’umar Rimin Zakara dake yankin Karamar Hukumar Ungogo a jihar Kano.
Alhaji Aminu Ado Bayero ya bayyanawa shugaban kasar damuwarsa matuka bisa yadda al’ummar suka shiga damuwa kan yadda aka samu rasa rayuka da dukiyoyi da kuma yadda wasu suka samu jikkata.
Shugaban ya tabbatarwa da Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero cewa za’ayi duk mai yuwuwa domin ganin an warware takaddamar tareda tabbatar musu da matsugunansu.
Gwamnatin Kano ta haramtawa yan kwangila zuwa ma’aikatar kananan hukumomi ta jihar – Kwamishina
Shugaba Tinubu ya nuna alhininsa tareda jajantawa mai martaba sarkin bisa abunda ya samu al’umarsa inda ya yabawa sarkin kan yadda ya damu da damuwar al’umar jihar Kano.
Wannan ziyara dai da mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya kai zuwa wajan shugaban Kasar bata da wata nasaba da tafiyar da Sunusi Lamido yayi zuwa Abuja kamar yadda wasu a kafafan sada zumunta na zamani ke yadawa.