Daga Rukayya Abdullahi Maida
Majalisar zartaswar jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf, ta amince da kashe kudi kimain Naira 8,199,635,732.07 domin gudanar da wasu manyan ayyuka 15 a fadin jihar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa Kadaura24, bayan kammala taron majalisar zartarwa karo na 24 da aka gudanar a gidan gwamnatin Kano ranar Laraba.
Ga rabe-raben yadda za a kashe kudaden:
• An ware Naira 2,737,518,204.96 domin yin gini mai hawa daya da ya kunshi ajujuwa hudu a makarantun dake kananan hukumomin jihar 44.
• Majalisar ta amince a kashe Naira 2,311,388,177.70 don karasa titi mai hannu biyu da ya tashi daga rawul din gidan gwamnati zuwa Lodge Road, Race Course Road, da Daula Hotel Roundabout, tare da ƙarin wasu ayyukan da suka kunshi titin asibitin Nasarawa, titin Dawaki, titin Lugard, da titin Dawaki.
• An ware Naira 1,870,814,360.10 domin gyaran dakin taro na Africa House da ayyukan tuntuba a gidan gwamnati.
• An ware N1,213,400,000 domin samar da lita 479 na dizal na watan Satumba zuwa Disamba 2024 da lita 16,000 na fetur ga gidan ruwa na Challawa a watan Satumba 2024.
Sulhunta Kwankwaso da Ganduje zai amfanar da Kano da Kanawa – Musa Iliyasu Kwankwaso
• An amince da kashe N790,757,887.93 don biyan basussukan da KEDCO ke bin gwamnatin jihar.
• An ware N378,711,009.60 domin biyan masu kai abinci ga makarantun kwana na satin farko da na biyu na zangon karatu na biyu da ke gudana.
• Naira 303,687,500.00 ne aka ware domin buga wasu muhimman takardun tsaro da Hukumar Bugawa da sabunta kudi ta Najeriya ta yi wa ma’aikatar kasa da tsare-tsare ta jihar.
• An amince da kashe Naira 117,346,156.28 domin gina Kauyen Doga da ke Karamar Hukumar Gabasawa.
• An ware Naira 482,827,622.22 don kammalawa da samar da fitilun titi masu amfani da hasken rana a titin 5 kilomita na Dawakin Tofa.
• An amince da Naira 568,584,750.00 don siyan babura 300 ga malaman gona dake aiki a Hukumar KNARDA.
• An ware Naira 17,253,832.00 domin samar da karamin shirin noman rani a mataki na farko a fadin jihar.