Yaki da Azzalumai: Gwamnan Kano Abba Gida Gida Ya Zare Takobi a Garin Zarewa

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

A yayin kaddamar da aikin titi mai tsawon kilomita tara, Gwamna jahar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida Gida, ya zare takobi wanda hakan ke nufi shirin sa na yakar azzalumai mamiya jihar.

Gwamna wanda ya yaba da kyautar kwafin Al’qur’ani bugun hannu da kuma felleliyar takobi daga hannu Dr. Ishaq Falalu Zarewa a madadin al’ummar yankin bisa kammala aikin titin da ya tashi daga Fulatan zuwa Zarewa da kuma wanda ya taso daga Danguzuri zuwa Zarewa mai tsawon kilomita tare, ya ce daga yau tsai kara damara wajen yaki da cin hanci da rashawa, zalunci da cutar da al’ummar jahar Kano.

InShot 20250115 195118875
Talla

“Mun samar wa wannan tituna ne saboda bunkasa hada hadar kasuwanci da habaka harkar noma ta domin a wannan yanki” a cewar Gwamnan Kano

Wannan dai shi ne karu na uku da Gwamnan ya fito fili ya nuna shirin sa na yakar masu shirin tada fitina a jahar ta Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Abubakar Bichi ya bada gudumawar motocin bas 13 ga jami’o’in Kano da taraktoci 11 ga yan mazabarsa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar...

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...