Daga Aminu Umar Sarki
Majalisar karamar hukumar Taurani ta sha alwashin tallafawa kungiyar tsofaffin daliban makarantar koyar da harshen larabci ta Kano (S A S) yan aji na shekarar 2005.
Mataimakin shugaban hukumar karbar Khalid Ayuba yasayyadi shi ne ya bayyana hakan lokacin da shugaban kungiyar suka Kai masa ziyarar taya shi murnar samun mukaminnasa.
Bayan ya nuna farin cikinsa dangane da ziyara ya ba su tabbacin kofarsa a bude take domin tallafawa kungiyar a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.

” Babu shakka na ji dadin wannan ziyarar saboda na ga wadanda na dade ban gan su ba, kuma Ina fatan lokaci zuwa lokaci za mu rika irin Wannan saduwar domin sada zumunci”.
Zargin cin zarafi: Ƴansanda sun kama hadimin Gwamnan Kano
Da yake jawabin shugaban kungiyar Barr. Adamu Muhammad Danfulani aji (2005) ya ce sun kai ziyarar ne domin taya murna ga daya daga cikin membobin kungiyar wanda ya sami mukamin mataimakin shugaban karamar hukumar Tarauni.
” Mun kawo maka wannan ziyarar ne domin taya ka murnar mukamin da ka samu , sannan mu sada zumunci saboda gaba dayanmu yau tare muka yi karatu yanzu kuma kowa yana harkokinsu, don haka muka ga dacewar mu zo don taya junanmu murnar”.