Sulhunta Kwankwaso da Ganduje zai amfanar da Kano da Kanawa – Musa Iliyasu Kwankwaso

Date:

 

 

Babban Daraktan kudi na hukumar raya kogunan Hadeja-Jama’are Musa Iliyasu Kwankwaso ya ce yana goyon bayan a sami sulhu tsakanin tsofaffin gwamnonin jihar Kano Kwankwaso, Ganduje, Shekarau da Kabiru Gaya.

” Tabbas sulhunta wadannan mutane zai taimakawa jihar Kano ta sami cigaba, wanda duk al’ummar jihar za su yi alfahari da shi, don haka sulhuntasu abu ne mai kyau”.

Musa Iliyasu Kwankwaso ya bayyana hakan yayin wata ganawa da yayi da jaridar Kadaura24 ranar laraba.

InShot 20250115 195118875
Talla

Ya ce akwai takaici yadda ake mayar da Kano baya ta hanyar soke wani abun alkhairi da daya daga cikinsu ya yiwa jihar Kano komi yadda al’umma suke amfana da aikin.

Zargin cin zarafi: Ƴansanda sun kama hadimin Gwamnan Kano

” So muke tsofaffin gwamnonin su rika hada kansu wajen daukar wasu matakai da zasu inganta rayuwar al’umma, sannan su amince a junansu cewa duk wanda ya sanya hannu akan wani aiki da zai amfanar da al’umma Kar wani ya zo saboda sabanin Siyasa a soke aiki”.

Ya ce dukkanin tsofaffin gwamnoni sun haura shekaru 65 don haka lokaci ya yi da ya kamata su hada hannu waje guda don ciyar da jihar Kano gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dr. Kabiru Getso Ya Mika Ta’aziyya Ga Iyalan Buhari

Daga Rahama Umar Gwaru   Tsohon kwamishinan ma'aikatun lafiya da muhalli...

Gwamnatin tarayya ta ayyana Ranar hutu saboda rasuwar Buhari

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ayyana Talata, 15 ga watan...

Injiniya Iliyasu Usman Salihu ya zama Jakadan zaman Lafiya na Africa

    Injiniya Ilyasu Uasman Salihu, Manajan Darakta na Sadex Engineering...

Halin da ake ciki game da shirye-shiryen jana’izar Buhari

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya bayayna cewa sai...