Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III ya ba da umarnin a fara duban jinjirin watan sha’aban a gobe laraba.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da shugaban kwamitin harkokin addinin musulunci Farfesa Sambo Wali Junaidu ya sanyawa hannu kuma aka raba manema labarai a sokoto.
Yanzu-yanzu: Gwamnan Kano ya yi sabbin nade-naden Mukamai
Sarkin Musulmin ya ce duk wanda ya ga watan ya kai rahoton zuwa ga mai unguwarsu ko dagaci domin sanar da fadar Sarkin Musulmin don sanar da ganin watan a hukumance.
Ganin watan na sha’aban dai shi ke nuna cewa watan Ramadan ya karo, domin a kalandar addinin musulunci daga watan sha’aban sai Ramadan Wanda al’ummar Musulmin duniya suke gudanar da ibadar azumi a cikinsa.