Rikicin Masarauta: Gwamnatin Kano ta Bayyana Matsayarta Kan Hukuncin Kotu

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano kuma Babban Lauyan Gwamnati, Haruna Isa Dederi, ya bayyana cewa hukuncin da Kotun Daukaka Kara, reshen Abuja, ta yanke kan takaddamar sarauta bai soke mayar da Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano na 16 ba.

Da ya ke jawabi ga manema labarai, Dederi ya jaddada cewa hukuncin Kotun Daukaka Kara na ranar 10 ga Janairu, 2025, ya tabbatar da ikon gwamnatin jihar na mayar da Sanusi kan karagar mulki.

Ya bayyana cewa kawai Kotun Koli ce ke da ikon sauya wannan hukunci.

InShot 20250309 102403344
Talla

Maganganunsa sun biyo bayan hukuncin da kotun ta yanke kan bukatar dakatar da aiwatar da hukuncin da Aminu Baba DanAgundi, daya daga cikin masu nada sarki masu biyayya ga Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ya shigar.

Rikicin Masarautar Kano: Kotu ta Sake Sabon Hukunci

Kotun ta umarci a ci gaba da tsayawa a inda ake har sai Kotun Koli ta yanke hukunci na karshe.

Dederi ya sake nanata cewa kotun daukaka kara ba ta soke hukuncinta na baya ba, sai dai kawai ta dakatar da aiwatar da shi har sai Kotun Koli ta yanke hukunci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dan Majalisar tarayya daga Kano ya fice daga jam’iyyar NNPP

Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Kano Municipal, Injiniya Sagir...

Abin mamaki: Barawo ya sace Motar dake cikin ayarin motocin gidan gwamnatin Kano

Wani barawon mota ya kutsa cikin gidan gwamnatin jihar...

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...