Daga Maryam Muhammad Ibrahim
Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince da nada Ibrahim Adam a matsayin mai bashi shawara ta musamman a kan harkokin yada labarai.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa Kadaura24.

Ibrahim Adam, matashi ne mai kimanin shekaru 32 ya yi digirinsa a jami’ar Bayero inda ya karanci kimiyar Siyasa (Political Science), yana daga cikin matasan da suke yada manufofin gwamnatin jihar Kano.
Sarkin Musulmi ya bayar da umarnin fara neman watan sha’aban a Nigeria
A baya dai ya zama hadimin Alhaji Abba Kabir Yusuf lokacin yana matsayin dan takarar gwamnan Kano daga shekara ta 2020 zuwa 2022, daga baya kuma ya koma aiki a matsayin PA na Rabiu Musa Kwankwaso.
Gwamnan ya taya Ibrahim Adam murna, sannan ya bukaci ya yi amfani da kwarewarsa wajen cigaban gwamnatin jihar Kano.