Kaso 30% ne kacal na mata ke haihuwa a asibiti – Gwamnatin Kano

Date:

Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano, Dakta Abubakar Labaran Yusuf, ya bayyana damuwarsa game da yadda ya ce kashi 30 ne kacal na mata a Jihar Kano ne ke haihuwa a asibiti, wani al’amari da ke bada gudunmawa wajen yawaitar mace-macen mata masu juna biyu a Jihar.

Ya jaddada cewa yawan mace-macen mata masu juna biyu a Najeriya ba abin abinda za a amince dashi ba ne.

InShot 20250115 195118875
Talla

Dakta Yusuf ya yi wannan bayani ne a jiya Litinin yayin wani taron bita da aka gudanar a Bristol Palace a Kano mai taken “Matakin Rage Mace-Macen Mata Masu Juna Biyu da Jarirai.”

Jaridar Tribune ta rawaito Kwamishinan na bayyana cewa, “Dole ne mu haɗa kai domin tabbatar da cikar burin gwamnatin tarayya na rage mace-macen mata masu juna biyu a kasar nan.

Tafiyar Kwankwasiyya a wajena tamkar ibada ce – Abubakar Adamu Rano

“Jihar Kano tana da muhimmanci sosai idan aka yi la’akari da alamu na bangaren kiwon lafiya da kuma matsalolin da ke addabar wannan bangare.

“Domin Kano, wacce ita ce jiha mafi yawan jama’a a kasar, ana samun yawan mace-macen mata masu juna biyu da jarirai, wanda ya hana ni da gwamna samun barci tun lokacin da muka hau kan mulki,” in ji Yusuf.

A cewar Kwamishinan Lafiya, gwamnatin Jihar Kano a kokarinta ta kirkiro da tsarin bayar da kulawar haihuwa kyauta ga mata masu juna biyu tare da samar da kayan aiki ga sama da cibiyoyin kiwon lafiya 60 da kuma cibiyoyin kula da lafiya na matakin farko guda 63.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamna Abba Ya Sanya Hannu Kan Dokar Kafa Gaya Polytechnic

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sanya...

Sojoji sun mikawa Tinubu Shawarwari yadda za a kawo karshen matsalar tsaron Nigeria

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya karɓi rahoton dakarun sojan...

Shugaba Tinubu ya sake nada Buba Marwa a matsayin shugaban NDLEA

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake tabbatar da nadin...

Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa Ya Koma Jam’iyyar APC a Hukumance

Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar...