Rikicin Sarautar Kano: Ana neman yi mana mulkin-mallaka da katsalandan – Kwankwaso

Date:

 

Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma jagoan jam’iyyar NNPP Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce daga ɓangaren Legs a ke yunƙurin mamaye wasu sassa na ƙasar, musamman Kano.

Kwankwaso ya yi ikirarin cewa Lagos na tsoma baki a harkokin cikin gida na Kano, musamman masarautar Kano.

Talla

Ya bayyana waɗannan zarge-zargen ne yayin da ya gudanar da jawabi a bikin yaye daliban Jami’ar Skyline da ke Kano a jiya Lahadi.

Da ya ke nuna damuwarsa kan abin da ya kira yin katsalandan, Kwankwaso ya yi gargadi kan matakan da za su iya tauye ‘yancin kai da al’adun gargajiya na sauran jihohi.

Gwamnan Kano ya kashe sama da Naira Biliyan 1 wajen inganta harkokin kiwon lafiya a jihar

“Yau, muna ganin a fili akwai gagarumin yunƙuri daga ɓangaren Legas na neman mallakar wannan yanki. Lagos ba za ta bari mu zaɓi Sarkinmu ba; a maimakon haka, suna son kakaba mana Sarkinsu a Kano,” in ji shi.

Idan za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito ana cigaba da dambarwar masarautar Kano tun lokacin da gwamnatin jihar kano ta bayyana tsige Alhaji Aminu Ado Bayero tare da bayyana dawo da Malam Muhammad Sanusi II a matsayin Sarkin kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...