Gwamnan Kano ya kashe sama da Naira Biliyan 1 wajen inganta harkokin kiwon lafiya a jihar

Date:

Daga Sani Idris Maiwaya

 

Gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf yana jagorantar gagarumin kawiy sauyi a fannin kiwon lafiya, ta hanyar kashe magudan kudade da nufin inganta ababen more rayuwa da walwalar ma’aikatan lafiya a fadin jihar.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Talata .

Sunusi Dawakin Tofa ya bayyana cewa majalisar zartarwar jihar ta amince da kashe kudi sama da Naira biliyan 1 ga fannin a taron majalisar karo na 15 da aka gudanar a gidan gwamnati.

“Wadannan tsare-tsare sun nuna irin kudirin gwamnan na inganta harkokin kiwon lafiya don kyautata rayuwar mazauna Kano a matsayin fanni na biyu da gwamnatinsa ta fi baiwa fifiko”.

Sunaye da Dalilin da suka sa aka dakatar da alkalai 3 a Kano

Ya ce gwamnan ya dauki batun haihuwa da muhimmanci Inda ya amince da ware Naira miliyan 165 don siyan muhimman magunguna da kayan karbar haihuwa ga matan da jariransu kyauta tun daga farkon shekara ta 2024.

Wannan ya nuna yadda Gwamnan ya ke damuwa da al’amuran da suka shafi mata, inda yace wanna mataki da gwamnan ya dauka ya taimaka matuka wajen rage mace-macen mata da kananan yara a jihar.

Gwamnatin Gwamna Yusuf ta kuma dauki kwararan matakai na ciyar da kayiyyakin da ake amfani da su a bangaren kiwon lafiya gaba. Inda aka ware wani kaso mai tsoka don kammalawa da haɓaka mahimman wuraren kiwon lafiya a jihar.

Gwamnan ya sake bayar da kwangilar kammala kwalejin koyon aikin jinya da ungozoma da ke Madobi da jarin Naira miliyan 57.

Kashim Shettima Ya Gargadi Gwamnan Sakoto Kan Tsige Sarkin Musulmi

Wannan yunƙuri na nufin haɓaka ilimin aikin jinya da samar da ƙwararrun jami’an kiwon lafiya.

An Kammala aikin wani Asibiti da ke Kadawa a Karamar Hukumar Gwale, wanda aka kashe Naira miliyan 61.8 tare da samar da kayan aiki don al’ummar yankin da makotansu su sami damar zuwa don kula da lafiyar su cikin sauki.

An shirya tsaf domin gyara D-ward na Asibitin Kwararru na Murtala Muhammed da ke Kano, domin kafa sashin kula da masu sikila na, inda aka ware Naira miliyan 81.6 domin gudanar da aikin.

Wannan rukunin zai ba da kulawar da ta dace ga marasa lafiya da ke fama da cutar sikila, wani muhimmin abin da ke damun lafiya .

Sanarwar ta ce, za a gyara asibitin masu fama da cututtuka na zana domin samar da sabuwar cibiyar yaki da cututtuka ta jihar Kano a cikinsa, inda aka ware Naira miliyan 64.8 domin yin aikin

Wannan wurin zai karfafa matakan da jihar ke dauka game da matsalolin kiwon lafiyar jama’a da kuma inganta yadda take kula da cututtuka masu yaduwa a jihar.

An ware karin Naira miliyan 28.5 domin ginawa da kuma gyara kwalejin koyon aikin jinya da ungozoma da ke Dambatta, tare da fadada damar karatu ga daliban da ke neman aikin jinya.

Waɗannan muhimman aiyukan da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi a fannin kiwon lafiya na Kano ya fito da manufarsa ta inganta lafiyar al’ummar jihar da.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zargin Almundahana: ICPC zata gurfanar da shugaban hukumar zabe ta Kano da wasu mutum biyu

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta (ICPC)...

Dalilin da ya hana ni zuwa Kano tarbar Tinubu – Ganduje

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa,...

Shugaban RATTAWU na Kano ya taya sabbin shugabannin kungiyar na kasa murna

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Shugaban kungiyar ma’aikatan rediyo, Talabijin da...

Dalilina na ziyartar gwamnan Kano Abba – Inuwa Waya

Daga Rahama Umar Kwaru Tsohon Wanda ya nemi Zama Dan...