Daga Aliyu Danbala Gwarzo
Mataimakin kakakin Majalisar Wakilai ta Nigeriya, Mista Philip Agbese, ya bayyana cewa wasu gwamnonin jihohi suna barazanar hana ‘yan majalisar tarayya sake tsayawa takara a zaben 2027, matukar ba su janye goyon bayansu ga kudurin sauya fasalin haraji na Shugaba Bola Tinubu da ke gaban majalisar tarayya don tattaunawa ba.
Agbese ya kuma bayyana cewa ‘yan majalisar za su gana da Shugaban Kwamitin Shugaban Kasa kan Gyaran Haraji da Kudaden Shiga, Taiwo Oyedele, tare da wasu kwararrun masana haraji kan dokokin a yau Litinin.
Idan za a iya tunawa, a ranar 3 ga Satumba, 2024, Shugaban kasa ya tura daftarin kudirin gyaran dokoki hudu ga majalisar tarayya don tattaunawa, bayan shawarar kwamitin Oyedele.

Dokokin sun hada da Dokar Haraji ta Najeriya ta 2024, wadda ake sa ran zata sauya fasalin tattara haraji a kasar.
Sauran dokokin sun hada da ‘Dokar Kafa Hukumar Haraji ta Najeriya’, wadda za ta soke dokar Hukumar Haraji ta tarayya (FIRS) tare da kafa Hukumar Haraji ta Najeriya.
Rikicin Sarautar Kano: Ana neman yi mana mulkin-mallaka da katsalandan – Kwankwaso
Akwai kuma ‘Dokar Kafa Kotun Hadin Gwiwa Kan Haraji’, wadda za ta kafa kotun haraji da zata ringa bayarda hukunci kan dambarwar haraji idan ta taso.
Sai dai, gwamnonin jihohi 36 na kasar nan sun nemi a janye wadannan kudirori, suna masu ikirarin cewa akwai bukatar karin tattaunawa da kuma jin ra’ayoyin jama’a kafin yin doka akan sauye-sauyen.
Sai dai,Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi watsi da shawarar gwamnonin, yana jaddada cewa majalisar Dattijai da talwararta ta wakilai ne kadai ke da hakkin amincewa ko akasin haka ga kudirin dokokin.