Daga Rahama Umar Kwaru
Wani matashi mai suna Yusuf Garba, ɗan kimanin shekaru 35 a jihar Kano ya daɓa wa kansa wuƙa, inda haka yayi sanadiyyar mutuwarsa Sakamakon sauraron kiɗan gangi.
Rundunar ’yan sandan Kano ta ce matashin ɗan garin Ɓutu-ɓutu da ke Ƙaramar Hukumar Rimin Gado ya daɓawa kansa wuƙa har lahira bayan da ya kunna kiɗan gangi.

Kakakin rundunar, Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana a shafinsa na Facebook, cewa matashin ya koma ga Mahaliccinsa ne bayan daɓawa kansa wuƙa a ciki da ƙafa, dalilin shaukin kiɗan da ya ɗebe shi.
Inganta Ilimi: Jam’iyyar adawa ta YPP ta Yabawa Gwamnan Jihar Kano
Ga sakon da Kiyawa ya wallafa
SHAUKIN KIDAN GANGI
” Yusuf Garba, dan shekaru 35 dake Garin Butu Butu, Karamar Hukumar Rimin Gado, Jihar Kano, ya kunna kidan gangi a waya, wanda kidan ya zabureshi da cakawa kansa wuka a kafa da ciki har lahira. Jama’a muna kiyaye rayuka da lafiyarmu”.