Daga Sharifiya Abubakar
Kungiyar Mawallafa jaridun yanar Gizo Ta The Association of Online Media Guild ASSOMEG ta mika sakon ta’aziyya ga mai magana da yawun gwamnan jihar kano Malam Sanusi Bature, bisa rasuwar dansa Sadiq Sanusi Bature wanda ya rasu ranar laraba yana da shakaru 15.

Wannan babban rashi ne da dukkan mu Mawallafa Jaridun Yanar Gizo mu ke ji, kuma muna cikin baƙin ciki da iyali ke jurewa a cikin wannan mawuyacin lokaci.
Ba fashi za mu gudanar da zaben kananan hukumomin Kano gobe Asabar. KANSIEC
Malam Sanusi Bature ya kasance babban abokin tarayya kuma mai bayar da shawarwari a fagen yada labarai, kuma tunaninmu da addu’o’inmu suna tare da shi, da iyalansa, da masoyansa.
A madadin daukacin membobin mu, Kungiyar ASSOMEG na mika sakon ta’aziyya ga Malam Bature da iyalansa.

Muna addu’ar Allah ya basu ikon jure wannan rashi da ba za a iya maye gurbinsu da shi ba.