Daga Rukayya Abdullahi Maida
Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya ce bai halarci ziyarar ta’aziyyar da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kai Kano a ranar Juma’a ba, sakamakon wasu sabgogi da yake yi a Landan, wanda ya fara kwanaki biyar bayan murabus dinsa daga shugabancin jam’iyyar.
Da yake karin haske game da lamarin, Malam Muhammad Garba, tsohon shugaban ma’aikatan ofishin shugaban jam’iyyar APC na kasa, ya ce sabanin rade-radin da ake yadawa a kafafen yada labarai cewa Dr. Ganduje ba shi da lafiya ko kuma da gangan aka cire shi daga tawagar shugaban kasar, Ganduje ya tafi Landan ne domin wasu sabgoginsa na kashin kansa un Kafin a Sanya ranar.

Muhammad Garba ya bayyana cewa shugaba Tinubu, ya kawo ziyarar ne Kano domin yin ta’aziyya ga iyalan marigayi hamshakin dan kasuwa, Alhaji Aminu Dantata, Wanda kuma an sanar da Ganduje cewa Tinubu zai zo Kano, amma abin takaici duk da kokarin da aka yi na sake tsara jadawalin jirgin da Gandujen zai dawo Nigeria Amma hakan ya ci tura.
Dalilina na ziyartar gwamnan Kano Abba – Inuwa Waya
Sai dai duk da kasancewar Dr. Ganduje a kasar waje, kusan kowacce sa’a daya sai ta tuntubi manyan jagororin jam’iyyar da suka hada da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin da kuma shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas, domin tabbatar da gudanar da ziyarar shugaban kasar cikin nasara.
Garba ya jaddada cewa murabus din Dr. Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar APC na kasa ko kadan ba zai shafi kyakykyawar alaka da ta dade tsakaninsa da shugaba Tinubu ba, dankon zumunci da aka gina tsawon shekaru na mutunta juna yana nan.