Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta (ICPC) ta ce za ta gurfanar da Shugaban Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kano (KANSIEC), Farfesa Sani Lawan Malumfashi, tare da Sakataren hukumar, Anas Muhammed Mustapha, da Daraktan Kuɗi na hukumar, Ado Garba, kan zargin wanke fiye da naira biliyan ɗaya.
Za a fara gurfanar da su ne a ranar Litinin, 21 ga watan Yulin 2025, a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.
A cewar hukumar ICPC, ana zargin waɗanda ake tuhumar da haɗa baki a tsakanin watan Nuwamba zuwa Disamba na shekarar 2024 wajen aikata almundahanar kudin, wanda hakan ya saba wa dokokin yaƙi da cin hanci.

Binciken hukumar ya gano cewa an fitar da fiye da naira biliyan ɗaya daga asusun hukumar KANSIEC da ke bankin Unity zuwa kamfanin SLM Agro Global Farm, wanda ba shi da kowace irin alaƙa da hukumar ta KANSIEC.
Dalilin da ya hana ni zuwa Kano tarbar Tinubu – Ganduje
Ko da yake wadanda ake zargin sun ce kuɗin anyi amfani dasu wajen biya ma’aikatan wucin gadi da suka yi aikin zabe a nan Kano, sai dai hukumar ICPC ta bayyana cewa wannan bayani ya saba da takardun banki da ƙa’idar kashe kuɗi da aka samu.
Haka kuma an gano wasu kura-kurai a kasafin kuɗin zaɓe, ciki har da naira miliyan 20 da aka ce an kashe wajen tantance ’yan takara a mazabu 484 na Kano, duk da cewa tantancewar ta gudana ne a ofishin hukumar da ke Kano.