NiMet ta bayyana jihohin da za a kwana uku ana ruwa da tsawa

Date:

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi hasashen samun tsawa da ruwan sama daga Laraba zuwa Juma’a a faɗin Najeriya.

A wata sanarwa kan yanayi da hukumar ta fitar ranra Talata, ta ce ana sa ran samun tsawa a wasu sassan jihohin Borno, Adamawa, Taraba, Yobe, Katsina, Sokoto da kuma Kaduna ranar Laraba.

NiMet ta ce za a kuma samu tsawa a wasu ɓangarorin jihohoin Kano, Katsina, Kaduna, Zamfara, Kebbi da kuma Jigawa da rana da kuma yammaci.

Asibitin Best Choice Ya Kaddamar Da Sabuwar Na’urar Jarirai Ta (Jaundice) Irinta Ta Farko A Arewacin Najeriya

“A arewa ta tsakiya, ana sa ran samun tsawa a Abuja, babban birnin ƙasar da Nasarawa da kuma jihar Neja a ranar Laraban,” in ji NiMet.

Jerin sunayen yan takara 38 da NNPP ta tsayar a zaɓen shugabannin kananan hukumomin Kano

Hukumar ta ƙara da cewa a yankin kudancin ƙasar ma za a fuskanci tsawa da ruwan sama a jihohin Oyo da Osun da Ekiti da Ogun da Ondo da Lagos da Edo da Delta da Cross River da kuma Akwa Ibom daga Laraba zuwa Juma’a.

Hukumar ta NiMet ta kuma ce za a samu iska mai ƙarfi kafin saukar ruwan saman a yankuna da dama, inda ta ja hankalin jama’a cewa su ɗauki matakan kariya da hukumomi suka fitar domin kare kansu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...