Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi hasashen samun tsawa da ruwan sama daga Laraba zuwa Juma’a a faΙin Najeriya.
A wata sanarwa kan yanayi da hukumar ta fitar ranra Talata, ta ce ana sa ran samun tsawa a wasu sassan jihohin Borno, Adamawa, Taraba, Yobe, Katsina, Sokoto da kuma Kaduna ranar Laraba.
NiMet ta ce za a kuma samu tsawa a wasu Ιangarorin jihohoin Kano, Katsina, Kaduna, Zamfara, Kebbi da kuma Jigawa da rana da kuma yammaci.
“A arewa ta tsakiya, ana sa ran samun tsawa a Abuja, babban birnin Ζasar da Nasarawa da kuma jihar Neja a ranar Laraban,” in ji NiMet.
Jerin sunayen yan takara 38 da NNPP ta tsayar a zaΙen shugabannin kananan hukumomin Kano
Hukumar ta Ζara da cewa a yankin kudancin Ζasar ma za a fuskanci tsawa da ruwan sama a jihohin Oyo da Osun da Ekiti da Ogun da Ondo da Lagos da Edo da Delta da Cross River da kuma Akwa Ibom daga Laraba zuwa Juma’a.
Hukumar ta NiMet ta kuma ce za a samu iska mai Ζarfi kafin saukar ruwan saman a yankuna da dama, inda ta ja hankalin jama’a cewa su Ιauki matakan kariya da hukumomi suka fitar domin kare kansu.