Da dumi-dumi: Rarara Ya Dauki Nauyin Aikin Wani Titi a Jihar Kano

Date:

Daga  Hafsat Abdullahi Muhammad

 

Shahararren mawakin siyasar nan Alhaji Dauda Adamu Abdullahi Kahutu Rarara ya dauki nauyin yin aikin titin Darmanawa Police Station zuwa Gandun Sarki har zuwa makarantar Firamare dake karamar hukumar Tarauni a jihar Kano.

A jawabinsa yayin kaddamar da aikin titin Rarara Yace ya dauki nauyin yin aikin titin ne saboda muhimmancinsa ga al’ummar yankin da kuma kokarin sa na ganin ya ba da ta gundunmawar wajen cikin jihar kano.

” Idan Allah ya ba ka dama ya kamata ka taimaki mutanen da Kuke tare da su da haka Ake samun cigaba a ko’ina a duniya, don haka na ba da umarnin fara aikin nan take”. Inji Rarara

Asibitin Best Choice Ya Fara Kula da Masu Lalurar Mafitsara

Ya ce nan da Kwanaki goma za a kammala aikin, Inda ya ba da tabbacin za a yi aikin titin ne da inganci saboda a jima ana amfana da shi.

” An jima ana fuskantar matsala akan wannan titin to so nake waɗannan matsalolin su zamo tarihi, don haka muna bukatar gudunnawar al’ummar wannan yankin ko da da addu’o’ine”.

NiMet ta bayyana jihohin da za a kwana uku ana ruwa da tsawa

A nasa jawabinsa mai unguwar Darmanawa ya yabawa Rarara bisa aikin da ya dauki nauyin gudanarwa da kudin aljihunsa, inda ya al’ummar yankin sun jima suna shan wahala saboda lalacewar titin .

Ya ba da tabbacin za su cigaba da tallafawa da ba da hadin kai ga duk wanda yake da kudirin taimakawa al’umma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dr. Kabiru Getso Ya Mika Ta’aziyya Ga Iyalan Buhari

Daga Rahama Umar Gwaru   Tsohon kwamishinan ma'aikatun lafiya da muhalli...

Gwamnatin tarayya ta ayyana Ranar hutu saboda rasuwar Buhari

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ayyana Talata, 15 ga watan...

Injiniya Iliyasu Usman Salihu ya zama Jakadan zaman Lafiya na Africa

    Injiniya Ilyasu Uasman Salihu, Manajan Darakta na Sadex Engineering...

Halin da ake ciki game da shirye-shiryen jana’izar Buhari

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya bayayna cewa sai...