Asibitin Best Choice Ya Kaddamar Da Sabuwar Na’urar Jarirai Ta (Jaundice) Irinta Ta Farko A Arewacin Najeriya

Date:

Asibitin Best Choice Ya Kaddamar Da Sabuwar Na’urar Jarirai Ta (Jaundice) Irinta Ta Farko A Arewacin Najeriya

_”Hanyar Cigaban Arewacin Najeriya!”_

A wani yunƙuri na inganta kulada kiwon lafiya, Asibitin kwararru na Best Choice ya ɗauki gabaren kula da kiwon lafiyar jarirai tare da ƙaddamar da Sashin fasaha don kula da Lafiyar Jarirai da aka tsara don magance ciwon shawara da hana lalacewar kwakwalwar ga jarirai.

A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban Asibitin Auwal Muhammad Lawal, ya lura cewa na urar ita ce irin ta ta farko wanda kwararrun likitoci ke amfani da ita wajan juyen jini cikin fasaha don inganta sakamakon jiyya ga yara.

A nan bangaren Dr Abdulmalik Saminu ya bayyana cewa na’ura ce mai cike da fasaha dake ɗaukar nauyin fitowar haske kaso 70% na ban mamaki dake daidaita buƙatar ƙari ko juyen jini.

Zaɓen Kano: NDLEA ta fitar da sakamakon yan takara 20 da aka yiwa gwajin shan kwaya

Ya kara da cewa bullo da wannan na’ura ta zamani ya nuna wani gagarumin ci gaba ne da Asibitin Best Choice ya bullo da shi don kula da kiwon lafiyar jarirai.

Saminu yace sashin Kula da Lafiyar Jarirai na iya yin maganin ciwon shawara yadda ya kamata cikin kwarewa ba tare da daukan yin doguwar jinya ga iyalai ba da kuma saukin kashe kudade.

“Mun fahimci irin yadda iyaye ke faman shan wahala game da yanayin lafiyar kananan yara”.

Jerin sunayen yan takara 38 da NNPP ta tsayar a zaɓen shugabannin kananan hukumomin Kano

“Saboda haka ne muka mai da hankali kan wannan fasaha don sauƙaƙe nauyin da ke kan iyalai da kuma samar wa yara yanayi mafi kyawu, domin samun rayuwa mai kyau”. In Ji Auwal.

Shugaban Asibitin ya bayyana cewa na’urar ita ce irin ta ta farko a Arewacin Najeriya, kuma ta uku a fadin Najeriya, kuma tana ba da cikakkiyar kariya da maganin jiyya ga jarirai.

Dr. Abdulmalik Saminu, babban kwararre likita ne a fannin kiwon lafiya ya bayyana fatansa cewa wannan ci gaban zai kara karfafa matsayin asibitin Best Choice a matsayin jagora a fannin kula da kiwon lafiyar kananan yara, tare da baiwa iyalai kwarin gwiwa kan kula da ‘yan uwansu.

Saminu daga nan ya godewa mamallakin asibitin bisa namijin kokarin da yayi na samar da wannan wannan fasaha ta zamani duk da bala’in tsadarta.

Da wannan sashin Kula da Lafiyar Jarirai ne, iyalai da yan uwa ba sa buƙatar neman tafiya ƙasashen waje don neman magani, kamar yadda asibitin Best Choice ke ba da kulawa ta musamman a cikin gida.

Za ku iya samun Best Choice Specialist Hospital at Plot782/783 Aminu Kano Way
Tal’Udu Round About Kano State

Phone Numbers

+2349123453534
+2342082443318

Gmail address
Bestchoiceclinic@gmail.com

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...

Dalilin Kwankwaso na kin shiga Hadakar ADC

Jam'iyyar NNPP ta ce abin da ya sa ba...