Daga Sani Danbala Gwarzo
Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince da nadin sabbin sarakunan da zasu jagoranci masarautun Rano, Gaya da Kuma karaye a matsayin sarakuna masu daraja ta biyu.
Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya sanyawa hannu kuma ya aikowa kadaura24.
Sarakunan da aka nada sun hadar da Alhaji Muhammad Mahraz Karaye a matsayin Sarkin Karaye, wanda kafin nadin nasa shi ne hakimin karamar hukumar Rogo.
Yanzu-yanzu: Gwamnan Kano ya sanya hannu a sabuwar dokar karin masarautu
Sai Alhaji Muhammad Isa Umar a matsayin Sarkin Rano wanda kafin nadin nasa shi ne hakimin karamar hukumar Bunkure.
Sai kuma Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir Gaya a matsayin Sarkin Gaya wanda a baya shi ne tsohon Sarkin masarautar Gaya wadda aka rushe.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya hori sabbin sarakunan masu daraja ta biyu da su zamo masu hada kan al’umarsu da tabbatar da zaman lafiya da kuma bunkasa al’adu a masarautunsu daban daban.
Sanarwar tace nadin nasu ya fara aiki ne nan take.