Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya zargi gwamnatin da ta gabace shi da ɗaukar nauyin ‘yan daba a Kano.
Yayin da yake jawabi a gabanin taron majalisar zartarwar jihar da aka gudanar ranar Asabar a fadar gwamnatin jihar, Gwamnan Abba Kabir ya nuna damuwarsa kan halin taɓarɓarewar tsaro da jihar ke fuskanta, musamman harkar dabanci.
”Kowa ya sani kafin mu shigo gwamnati, waccan gwamnatin da ta shuɗe ita ce ke ɗaukar nauyin ‘yan daba, ita ce ke sa su suna yin abin da duk suka ga dama suna cutar da al’umma”, in ji gwamnan na Kano.
Rikicin Sarautar Kano: Yan Sanda Sun Dauki Bangare – Gwamnan Kano
Gwamnan ya kuma ce a lokacin yaƙin neman zaɓensa ya yi alƙawarin kakkaɓe matsalar daba a Kano.
Ya kuma ce bayan nasararsa a zaɓen gwamnatinsa ta yi ƙoƙarin daƙile matsalar.
Amma ya ce a cikin wata biyu da suka gabata wasu da ya kira ”maƙiyan jihar” suka maido da harkar daba.
Gwamnatin Kano ta Gargaɗi Al’umma Game da Amfani da Ruwan Sama
Inda ya yi zargin cewa wasu sun ɗauko hayar wasu ‘yan daba daga makwabtan jihohi domin su kawo wa zaman lafiyar jihar cikas.
Abba Kabir ya kuma yi barazanar fara kiran sunayen mutane da yake zargi da ɗaukar nauyin ‘yan daba a jihar.
Haka kuma gwamnan ya nuna damuwarsa kan yadda ya ce wasu na zuwa ofishin ‘yansanda domin fito da ‘yan daba idan hukuma ta kama su.
Inda ya yi barazanar cewa duk mutumin da gwamnatinsa ta sake samu da wannan laifi to za a gurfanar da shi a gaban kotu, domin yin bayanin dalilinsa na ɗaukar nauyin ‘yan daba a Kano.
A baya-bayan nan dai jihar Kano na fuskantar faɗace-faɗacen ‘yan daba, waɗanda ke cin karensu babu babbaka a wasu unguwannin jihar.