Daga Maryam Muhammad Ibrahim
Sheikh Saleh Al-Shaiba, babban mai kula da makullan Ka’aba mai tsarki ya rasu.
Haramain, shafin yanar gizon da ke ba da labarai da bayanai game da Masallacin Annabi da ke Madina da kuma Masallacin Harami da ke Makkah ya rawaito tabbatar da rasuwar Al-Shaiba a shafinsa na X a safiyar ranar Asabar.
Ya ce an gudanar da Janazar marigayin ne bayan Sallar Asubahin yau a Masallacin Harami, tare da binne shi a makabartar Al Mu’alla da ke Makkah.
Allah ya jikansa da rahama. Ameen
Kadaura24 ta rawaito cewa marigayin shi ne mutum na 109 daga Uthman ibn Talha (RA) sahabin Manzon Allah wanda ya fara zama mai kula da mabudin Ka’aba.