Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, AIG Usaini Gumel, ya bayyana dalilan da suka sa ‘yan sandan suka ki bin umarnin Gwamna Abba Yusuf na fitar da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero daga gidan sarki na Nassarawa.
Idan dai za a iya tunawa gwamna Yusuf a daren ranar Alhamis ta bakin babban mai shari’a na jihar kuma kwamishinan shari’a, Haruna Dederi, ya umurci CP da ya fitar da Sarkin Kano 15 daga gidan sarki na Nasarawa inda ya ke zaune .
Da yake magana a wata hira da jaridar The Punch ta wayar tarho a ranar Juma’a, kwamishinan ‘yan sandan ya ce bin umarnin fitar da sarkin da gwamnan ya bayar zai zama kamar tubka da warwara.
Gwamnatin Kano ta Gargaɗi Al’umma Game da Amfani da Ruwan Sama
A cewarsa, gwamnatin da ta ba da wannan umarni ta shigar da kara a babbar kotun jihar kan hukuncin korar wani, wanda kuma kotun zata zauna kan maganar a ranar Litinin 24 ga watan Yuni 2024.
“Rundunar ‘yan sanda ba za ta fitar da sarkin ba, domin ita wannan gwamnati ta shigar da kara a babbar kotun jihar kan hukuncin korar wanda zai zo a ranar Litinin, 24 ga watan Yuni, 2024.
“Don haka, idan muka bi wannan umarni, kamar mun yi yiwa kotu riga malam masallaci ne saboda ba mu san abin da zai faru a kotun ba,” a cewa kwamishinan.
Gwamnatin Kano ta baiwa yan sanda sabon umarni akan Sarki Aminu Ado Bayero
A halin da ake ciki dai an tsaurara matakan tsaro a kusa da gidan sarkin na Nasarawa inda a halin yanzu a nan sarki Aminu Ado Bayero yake.
Wakilin jaridar kadaura24 da ya ziyarci gidan sarkin na Nasarawa da safiyar wannan rana ta juma’a inda yace ya iske an kara Tsaurara matakan tsaro a kewayen gidan.
An dai lura cewa jami’an tsaro sun tare dukkanin manyan hanyoyi guda hudu da da za su Kai mutum zuwa karamar fadar, saboda har yanzu ‘yan sanda ba su fitar da sarkin da aka tsige ba kamar yadda Gwamna Yusuf ya umarta.
Duk da haka, yayin da CP din bai bi umarnin gwamna ba, har yanzu Sarkin da aka tsige yana cikin karamar fadar tare da hadimansa na masu gadin fadar da sauran magoya bayansa.