Daga Rahama Usman
Tsohon kwamishinan harkokin noma na jihar kano Dr. Yusuf Jibril JY ya bukaci gwamnatin jihar da ta bi umarnin kotun tarayya na tabbatar da dawo da Sarakunan Rano Gaya Bichi da Karaye.
” Muna da kyakykyawan yakinin gwamnatin za ta mutunta umarnin kotu saboda ta amfani hukuncin kotu don haka ita yafi dacewa ta mutunta umarnin don kiyaye doka da Oda”.
Yanzu-yanzu: Kotu ta Yanke Hukunci Kan Rikicin Sarautar Kano
Dr. Yusuf Jibril JY ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da jaridar kadaura24, jim kadan bayan hukuncin kotu.
Ya ce mutunta umarnin kotun zai kara fito da kimar gwamnatin, amma rashin bin umarnin kuma zai zubar da kimar gwamnatin a idon al’ummar jihar kano da kasa baki daya .
Dr. JY ya bukaci al’ummar jihar Kano da su gudanar da murnar dawo da Sarakunan su cikin kwanciyar hankali da lumana, ba tare da karya doka ba.
” Ina amfani da wannan dama wajen taya mai martaba Sarki Rano Alhaji Dr. Kabir Muhammad Inuwa, bisa dawo da shi kan karagarsa ta Sarautar Rano wadda aka ba cire shi ba bisa ka’ida ba”. A cewar Dr. JY