Sakon taya Murnar Zama Farfesa Daga Kungiyar Inuwa Kofar mata

Date:

Daga Khadija Abdullahi

Kungiyar bunkasa cigaban unguwar Kofar mata da kewaye mai taken (Inuwar unguwar Kofar mata) ta mika sakon taya murna ga Dr Bala Ado Kofar mata bisa daga darajarsa zuwa matakin Farfesa abangaren ilmin kanana da matsa kaitan sana’o’in dogaro dakai wato
(Professor of Entrepreneurial Studies ) da hukumar gudanarwar jamiar Bayero ta gudanar a makon jiya.

Kazalika kungiyar ta sake mika sakon taya murna ga
Dr. Lubabatu Bello Dan kadai bisa kaiwa ga matakin share faggen zama Farfesa a bangaran ilmin dokokin shari’un kasa masu zaman kansu dana kasuwanci wato (Associate Professor on private and commercial law) a jamiar Bayero dake nan Kano.

Bayanin hakan yana kunshe cikin sanarwar da sakataran yada labaran kungiyar Mal Usman Abdu Kofar mata ya fitar a madadin shugaban kugiyar Mal. Adamu Mararraba da sakataran kungiyar Alhaji Ado Musa Kofar mata (Adori).

Professor Bala Ado wanda dadadden malamine daya jima yana bada gudunmawa a bangaren habaka kananan sana’o’in dogaro dakai sashin ilmin bunkasa kananan sanaoi n jamiar Bayero dake nan yayinda Professor Lubabatu Bello Dankadai itama ta samu yabo a bangaren tallafawa matasa abangaren ilmi a jamiar ta Bayero.

Daga karshe kungiyar ta Inuwar Unguwar Kofar mata ta sake karfafar sabbin Farfesa biyu dasu kara azama akan kokarin da akasansu na ciyar da kasa Nigeria gaba abangaren ilmin da Allah ya fuwace musu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnan Kano ya Naɗa Ahmed Musa a Matsayin Janar Manaja na Kano Pillars

Daga Zakaria Adam Jigirya   Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir...

Yanzu:yanzu: Gwamnan kano ya yi sabbin nade-naden mukamai

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Gwamann jihar Kano Alhaji Abba Kabir...

Yara ɗalibai na fuskatar barazanar daina zuwa Makaranta a Hotoro saboda lalacewar hanya

Daga Isa Ahmad Getso   Al'umma da Malaman makaranta a unguwar...

Kotu ba da umarnin mayar da Natasha bakin aikinta

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci Majalisar...