Buhari Zai tafi Kasar Amuruka

Date:

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai tafi kasar Amurka ranar Lahadi domin halartar babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya a birnin New York.

Sanarwar da fadar shugaban ta fitar ta ce a ranar Talata 14 ga watan Satumba za a buɗe taron karo na 76 wanda zai mayar da hankali kan farfadowa daga annobar korona da sake gini mai ɗorewa da girmama haƙƙin ɗan Adam da kuma yadda za a raya Majalisar Ɗinkin Duniya.

A ranar Juma’a shugaba Buhari zai gabatar da jawabi a zauren majalisar, sannan zai keɓe da wasu shugabannin ƙasashe da na hukumomin ci gaban ƙasashen duniya.

Daga cikin tawagar shugaban da za su yi masa rakiya akwai ministan harakokin waje Geoffrey Onyeama da ministan shari’a Abubakar Malami da kuma karamin ministan muhalli Sharon Ikeazor.

Sanarwar ta ce sai a ranar Lahadi 26 ga watan Satumba ake sa ran shugaban zai dawo Najeriya

17 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...

Abdulmumin Kofa ya koma APC tare da bayyana goyon bayansa ga Tinubu

Abdulmumin Jibri Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru...

Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026

Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria ...