Daga Kamal Yahaya Zakaria
Shugaba Bola Tinubu ya nada Engr. Abubakar Momoh a matsayin Ministan ma’aikatar raya yankin Neja Delta.
Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da kakakin shugaban kasar, Ajuri Ngelale, ya fitar a daren Lahadi.

Ma”aikatar raya yankin Neja Delta ta bace a cikin jerin ma’aikatun da aka tura ministoci a makon jiya, lamarin da ya janyo cece-kuce.
Shugaban Mulkin Soji na Nijar ya bayyana lokacin da zasu mika Mulki ga farar hula
A ranar Asabar, kungiyar Pan Niger Delta Forum, PANDEF, ta sha alwashin yin watsi da duk wani yunkurin soke ma’aikatar Neja Delta.
Baya ga shigar yankin Neja Delta, shugaban ya kuma canzawa wasu ministocin ma’aikatu.
Adegboyega Oyetola, wanda da farko aka nada shi Ministan Sufuri, an mayar da shi Ma’aikatar albarkatun kasa, yayin da Bunmi Tunji-Ojo aka mayar da shi a matsayin Ministan Harkokin Cikin Gida.
Jaruma Aisha Humairah ta baiwa masoyanta masu son zuwa wajenta Shawara
Hon. Sa’idu Alkali ya zama Ministan Sufuri.
“Bugu da ƙari, Ministocin biyu a fannin Man Fetur da Gas yanzu suna zaune a Ma’aikatar Albarkatun Man Fetur ta Tarayya tare da sunayen kamar haka:
“(i) Sen. Heineken Lokpobiri shi ne Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur
(ii) Hon. Ekperipe Ekpo shine Hon. Karamin Ministan Gas da Albarkatun Man Fetur.”
Shugaban ya kuma amince da sauya sunan ma’aikatar muhalli da kula da zaizayar kasa ta tarayya zuwa ma’aikatar muhalli ta tarayya.
Sanarwar ta kara da cewa “Duk sauye-sauyen da aka ambata sun fara aiki ne nan take bisa umarnin shugaban kasa.”
A ranar Litinin ne dai za a rantsar da ministocin a fadar shugaban kasa da ke Abuja.