A Gaggauce: Fadar shugaban Kasa ta musanta murabus din Sakataren gwamnatin tarayya

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

Fadar shugaban Kasa ta musanta labarin da ake yadawa cewa George Akume ya ajiye aikinsa na Sakataren gwamnatin tarayya.

Kadaura24 ta rawaito A dare ranar asabar ne dai wasu mutane a shafukan sada zumunta suka rika yada cewa Wai George akume ya yi murabus daga mukaminsa na Sakataren gwamnatin tarayya.

InShot 20250309 102512486
Talla

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Kasa Bayo Onanuga ya fitar ya ce labarin na shi da tushe ballantana makama.

Ya ce Shugaban Kasa ba ma ya kasar ballantana a yi Maganar ya sauke wani ko ya nada wani inda ya bukaci al’umma da su yi watsi da labarin ba shi da tushe.

Gawuna ya mika ta’aziyyar rasuwar Alhaji Aminu Dantata

Sanarwar ta ce babu wani sabon sauyin mukami da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi, duk da cewa yana halartar taro a ƙasar Saint Lucia.

Ta ce rahoton da ke yawo game da sauya Akume labari ne na ƙarya da masu tayar da hankali suka kirkira.

Fadar Shugaban Ƙasa ta shawarci ’yan Najeriya da su yi watsi da labaran ƙarya da ake yaɗawa, tana mai jaddada cewa George Akume na ci gaba da kasancewa a matsayin SGF.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rasuwar Buhari: Majalisar Nigeria ta dakatar da duk aiyukanta

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Majalisar dokokin Nigeria ta dage zamanta...

Gwamnati ta baiwa ma’aikata hutu saboda rasuwar Muhammad Buhari

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gwamnatin jihar Katsina karkashin gwamna Umar...

Bayan tura Kashim ya taho da gawar Buhari, Tinubu ya ba da umarnin sassauta Tutar Nigeria

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bada umarnin ayi kasa...

Yanzu:yanzu: Tsohon shugaban Nigeria Buhari ya rasu

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un!!! Allah yayi wa tsohon shugaban...