Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
Gwamnatin jihar Kano ta ayyana gobe Laraba, 19 ga watan Yuli, 2023 a matsayin ranar hutun domin murnar shigowa sabuwar shekara ta Musulunci ta 1445.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kwamishinan yada labarai na jihar kano Baba Halilu Dantiye a madadin gwamna Abba Kabir Yusif.
Gwamnan wanda ya taya al’ummar musulmin duniya murnar zagayowar sabuwar shekara ta Musulunci, ya kuma bukaci ma’aikatan gwamnati da sauran al’ummar jihar da su yi addu’ar Allah ya kawo mana zaman lafiya da kwanciyar hankali tare da bunkasa tattalin arzikin jiharmu da kasa baki daya”.
Gwamnan Kano ya nada masu bashi shawara 15
Gwamnan ya kuma yi kira ga al’umma da su rika gudanar da rayuwarsu bisa koyarwar addinin Musulunci tare da yin koyi kyawawan dabi’u na kyautatawa da soyayya da kuma hakuri da juna kamar yadda Annabinmu Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi misali da shi.