Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Shugaban rukunin kamfanin man fetur na Najeriya NNPC , Mele Kyari, ya ce yanayin kasuwar man fetur ce tasa farashin man ya kai Naira 617.
Kyari ya bayyana haka ne a yammacin ranar Talata bayan ganawarsa da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Ya ce idan aka karkata akalar man fetur, hakikanin kasuwa zai sa farashin man fetur ya tashi a wasu lokutan, wani lokacin kuma yasa ya sauka.
Shekarar musulunci: Gwamnatin Kano ta bada hutu ga ma’aikata
Shugaban na NNPC, ya ce karin farashin man na kowace litar daga sama da N500 zuwa N617 ba batun karancin sa ba ne, yana mai tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa Nigeria na da wadataccen man kasa.
Kyari ya ce Najeriya na da wadataccen man da za’a iya yin kwanaki 32 amfani da shi ba tare da an sami karancin sa ba.
Kyari ya ce tawagar harkokin kasuwanci ta NNPCPL ce ke da alhakin daidaita farashin kuma ayarin zai “daidaita farashin daidai da yanayin da kasuwa ta nuna ”.
Ya ce, “Hakika abin da ke faruwa ke nan; wannan yana tabbatar da cewa kasuwa ta daidaita kanta ta yadda farashin zai tashi, wani lokacin ma yakan sauko”.
Kyari ya tabbatar wa ‘yan Nigeria cewa tashin farashin man fetur din ba shi da alaka da matsalar samar da man.