Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Hukumar karɓar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, ta kama tare da tsare kwamishinan ayyuka na tsohon gwamna Abdullahi Ganduje, Engr Idris Wada Saleh da wasu mutane biyar bisa zargin almundahanar Naira biliyan 1.
Majiyar Kadaura24, Solabase ta rawaito cewa an kama kwamishinan wanda kuma shi ne Manajan Darakta na Hukumar Kula da Titin Kano wato KARMA, da Babban Sakatare na Hukumar sayo kayiyyakin gwamnati, Mustapha Madaki Huguma, da Daraktan Kudi, sai kuma Daraktan Bincike da Tsare-tsare tare da wasu a ranar Litinin da yamma bisa zargin karkatar da sama da Naira biliyan 1 da aka yi wa kasafin gyaran wasu tituna guda 30 da magudanar ruwa a cikin birnin Kano .

Wata majiya a hukumar ta shaida wa Majiyar mu cewa an biya kudaden da aka cire a cikin asusun kamfanoni uku a ranar 25 ga Afrilu, 2023.
“Abin mamaki har hukumar sayowa da adana kayan gwamnati ta bayar da satifiket na rashin amincewa da kwangilar bayan an biya kudin kwanaki goma kafin ba da kwangilar, wanda hakan ya sabawa dokar sayan kaya ta jihar Kano ta 2021,” inji majiyar.
Sallah: Gwamnan Kano ya nemi afuwar Sarkin Gaya kan abun da ya faru a gidan gwamnati yau
“Kamfanonin na bogi suna dukkanin su suna da takardar rubutun wasiƙa guda ɗaya kuma ba tare da an San tartibin ofishin su ba.”
‘’Hukumar bin ka’idoji gwamnati ta ce ba a bayar da takardar shedar rashin amincewar ba, saboda hukumar kula da titinan Kano (KARMA) ta ce za a yi aikin gyaran hanyoyin ne ta hanyar aiki kai tsaye, amma takardun da aka basu suka karanta ba su nuna haka ba.
Kamfanonin sune North stone Construction Company Nig. Ltd, Arfat Multiresources Ltd da 1st Step Construction Ltd.
Kakakin hukumar Abba Kabir ya tabbatar wa majiyar mu cewa wadanda aka kama suna fuskantar tambayoyi kuma za a gurfanar da su a gaban kotu da zarar an kammala bincike.