Daga Aliyu Danbala Gwarzo
Shugaban ma’aikatan kananan hukumomi na jihar kano (NULGE), Kwamarat Abdullahi Muhd Gwarzo ya bukaci al’ummar musulmi da su yi amfani da wannan lokaci wajen yiwa kasar nan addu’o’in samun zaman lafiya da karuwar arziki.
“Nigeria tana cikin mawuyacin halin da ya kamata al’umma su Maida hankali wajen yiwa kasar addu’o’i musamman a wadannan kwanaki masu tarin albarka, sannan suma shugabanni su a yi musu addu’a don su sami damar sauke nauyin da aka dora musu”.
Ganduje ya Magantu kan dakatar da albashin ma’aikata dubu 10 da gwamnatin Kano ta yi
Shugaban kungiyar ta NULGE ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da babban mataimakinsa na musamman Jibril Yusuf (WALCOT) ya sanyawa hannu kuma aka aikowa Kadaura24 .
Ya bukaci ma’aikatan kananan hukumomin jihar kano da su baiwa Sabuwar gwamnatinn kano karkashin jagorancin Gwamna Engr. Abba Kabir Yusuf, hadin kai domin cigaban jihar kano.

Kwamarat Abdullahi Muhd Gwarzo yace yana taya kafatanan ma’aikatan kananan hukumomin jahar kano da kwamishinan kananan hukumomi na jihar kano, wanda shi ne mataimakin gwamna Kwamarat Aminu Abdusalam gwarzo.
Shugaban ma’aikatan kananan hukumomin na jihar kano (NULGE) wanda shi ne Matawallen Gwarzo ya mika sakon barka da sallah ga daukacin alummar musulmin duniya musamman ma’aikatan kananan hukumomin jihar kano.
Ya yi addu’ar Allah ya karbi ibadun Mahajjatan da Allah ya basu ikon sauke farali a bana, sannan ya bukaci wadanda Allah yasa sukai layya da su taimakawa wadanda basu yi ba don samun lada a wajen Allah.