Akwai yiwuwar Man fetur ya sake tashin gwauron zabi a Nigeria – IPMAN

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Ƙungiyar dillalan man fetur masu zaman kansu a Najeriya ta ce akwai yiwuwar nan da lokaci kaɗan farashin man fetur zai zarce naira 600 a kan kowace lita.

 

IPMAN ta ce hakan zai faru ne sanadiyyar rashin tabbas kan samuwar dala ga ƴan kasuwa masu shigo da tataccen man fetur daga ƙasashen waje.

Ganduje ya Magantu kan dakatar da albashin ma’aikata dubu 10 da gwamnatin Kano ta yi

Bayanai sun nuna cewa da zarar ‘yan kasuwa masu zaman kansu suka fara shigo da man fetur a wata mai kamawa, farashin litar mai zai haura sama a faɗin ƙasar.

Tallah

A lokacin da yake tabbatar wa BBC da wannan batu, shugaban ƙungiyar dillalan man fetur ɗin a yankin Arewacin Najeriya, Bashir Dan-Mallam ya ce dole ne sai gwamnati ta ɗauki matakan da suka dace domin hana faruwar hakan.

Dan-Mallam ya ce samuwar dalar a wadace ga ƴan kasuwa za ta hana hauhawar farashin na litar mai.

A yanzu dai kamfanin man fetur na ƙasar NNPC ya ce zai riƙa shiga da kashi 30% na man fetur ɗin da ƙasar ke buƙata, yayin da ƴan kasuwa za su shigar da sauran.

A ranar 29 ga watan Mayun 2023 ne shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur, wani lamari da ya haifar da tashin farashin litar man fetur a faɗin ƙasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Wata sabuwa: Sanata Barau Jibrin ya gana da Baffa Bichi da Muhd Diggol

Tsohon sakataren gwamnatin Jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi...

Rikicin Masarautar Kano: Kotu ta Sake Sabon Hukunci

A wani sabon yanayi na rikicin Masarautar Kano, Kotun...

Gidauniyar Aliko Dangote za ta rabawa ‘yan Najeriya miliyan daya shinkafa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gidauniyar Aliko Dangote ta raba buhunan...

Rufe Makarantu da azumi: Ministan Ilimi ba ta da ilimin harkokin mulki – Jafar Sani Bello

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano...