Daga Rukayya Abdullahi Maida
Amb. Dr. Yunusa Yusuf Hamza, Falakin Shinkafi, ya gudanar da rabon kayan Sallah da kayan abinchi ga akalla marayu sama da guda 100 a jihar kano.
” Dole ne mu tallafawa rayuwar wadanna yaran saboda, mutuwa ce ta raba su da Iyayen su, Kuma muma zata iya raba mu da namu ‘ya’yan, don hakan abun da muka aminta da shi shi ne dole ne mu tallafa musu don inganta rayuwar su, kamar yadda addinin musulunci ya koyar”. Inji Dr. Yunusa Yusuf
Gwamna Ganduje ya nada Surajo Umar Wudil a matsayin SSA
Da yake bayani yayin rabon kayan ga marayun da aka zabo daga sassa daban-daban a jihar kano, Falakin Shinkafin ya ce ya basu tallafin ne domin suma su gudanar da bikin Sallah cikin farin ciki kamar kowa.
Fatawa: Ya halatta ayi zakkar fidda kai da Taliya Kuskus ko Indomie – Mal Ibrahim Khalil
‘Idan Muna son ganin dai-dai a rayuwar mu to mu taimakawa marayu da abun da Allah ya hore mana, saboda Allah ba wai ya bamu abun da ya bamu bane kawai Saboda mu da ‘yan’yan mu, a’a ya bamu ne don kyautatawa bayinsa Masu karamin karfi”. A cewar Falakin Shinkafi
Falakin Shinkafi wanda kuma shi ne Jarman matasan arewa ya bukaci sauran masu rike da madafun Iko da masu hannu da shuni da su rika amfani da dukiyoyin su wajen taimakawa marayu da sauran masu karamin karfi.
Wasu daga cikin wadanda suka amfana da tallafin sun yabawa Falakin Shinkafi tare da yi masa addu’o’in samun nasara a rayuwar sa da kuma fatan gamawa lafiya.