Daga Sani Idris Maiwaya
Kwamitin karɓar mulki na NNPP na 2023 a jihar Kano ya gargadi daukacin shugabannin kananan hukumomi 44 da manyan ma’aikatan su da su guji bari a yi amfani da kudaden kananan hukumomin su ta hanyar data sabawa doka.
” Mun Sami labarin ana shirin amfani da kudaden kananan hukumomi wajen kammala zabuka a Inda basu kammala ba, a wasu kananan hukumomin a jihar kano, wanda yin hakan ba dai-dai bane Kuma ya sabawa doka.
Ganduje ya kore mu daga APC, mu kuma mu ka yi masa ritaya daga siyasar Kano – Abdulmumini Kofa
Shugaban kwamitin Dr. Abdullahi Bafa Bichi ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu kuma aka aikowa kadaura24.
Yace baza su lamunci yin almubazzaranci da dukiyoyin al’ummar jihar kano ba, don haka suke baiwa shugabannin kananan hukumomin da su guji yin hakan , domin gwamnati mai jiran gado bazata bari a ɗauki kudaden al’umma a yiwa wata jam’iyyar siyasa aiki ba .