‘Yan mata 20,000 da aka aurar bara sun haifi jarirai 10,000

Date:

Daga Maryam Abubakar Tukur

 

Fiye da ‘yan mata dubu 20,000 ne ‘yan shekara 15, aka aurar a cikin wata tara da suka gabata a ƙasar Iran, a cewar alƙaluman Cibiyar Ƙididdiga ta Ƙasar.

 

A cewar alƙaluma da jaridar intanet ta Etemad ta wallafa, an kuma samu “sakin aure 179 a cikin ‘yan matan ‘yan ƙasa da shekaru 15”.

 

Akwai ‘yan mata ‘yan ƙasa da shekaru 15 da suka haifi jarirai 1,085.

 

Cibiyar Ƙididdigar ta wallafa wannan rahoto ne a kan halin rayuwar zamantakewa da ta al’adar al’ummar Iran a cikin watanni ukun farkon shekara.

 

A cewar dokokin kula da hulɗar jama’a na Iran, shekarun aure ga ‘ya mace suna farawa ne daga 13, maza kuma daga shekara 15.

 

Haka zalika, ana iya aurar da mutum wanda shekarunsa ba su cika ƙa’ida ba, bisa doka amma da sharaɗin yardar mahaifi ko wani mai kula da shi sannan sai kotu ta amince.

 

Yunƙurin canza shekarun aure a majalisar dokokin Iran yana da dogon tarihi a ƙasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zargin Almundahana: ICPC zata gurfanar da shugaban hukumar zabe ta Kano da wasu mutum biyu

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta (ICPC)...

Dalilin da ya hana ni zuwa Kano tarbar Tinubu – Ganduje

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa,...

Shugaban RATTAWU na Kano ya taya sabbin shugabannin kungiyar na kasa murna

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Shugaban kungiyar ma’aikatan rediyo, Talabijin da...

Dalilina na ziyartar gwamnan Kano Abba – Inuwa Waya

Daga Rahama Umar Kwaru Tsohon Wanda ya nemi Zama Dan...