Kungiyar Ciyamomin kano ( ALGON) ta Gargadi Baffa Bichi kan shawarar da Abba Gida-gida ya ba su

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Kungiyar Shugabannin Kananan Hukumomin Jihar Kano ta jihar kano ya bukaci kwamitin karɓar mulki na jam’iyyar NNPP da su guji shiga ko yin zargi akan abun da basu da masaniya akai don inganta zaman lafiya a kano.

 

Hakan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Shugaban kungiyar shugabannin kananan hukumomin jihar kano Hon. Muhd Baffa Takai Kuma aka rabawa manema labarai a kano.

Kammala zaben 2023: Abba Gida-gida ya baiwa shugabannin kananan hukumomin Kano shawara

 

” An jawo hankalin kungiyar mu ta ALGON cewa kwamitin karɓar mulki Yana zargin za’a yi amfani da kudaden kananan hukumomi yayi Kara zabuka a wasu kananan hukumomin jihar nan, babu shakka wannan zargi bashi da tushe ballantana makama”. Inji sanarwar

Ganduje ya kore mu daga APC, mu kuma mu ka yi masa ritaya daga siyasar Kano – Abdulmumini Kofa

 

” Dama wanann ba sabon abu bane domin ko a shekaru bayan lokacin da Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso zai mika mulki ga gwamnatin da ta gaje shi, sai da aka zarge shi da daukar Naira Miliyan 70 a kananan hukumomin 44 wanda kuma har yanzu maganar tana gaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa”.

 

Sanarwar ta bukaci Dr. Baffa Bichi wanda shi ne yasa hannu a sanarwar da aka zarge su da ya daina tsoma baki akan abun da bashi da hurumi, ya maida hankali kan aikin da aka dora masa, don tabbatar da zaman lafiya a jihar kano.

Wannan ita ce wasikar ta ALGON Kano

Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito kwamitin karɓar mulki na jam’iyyar NNPP ya baiwa shugabannin kananan hukumomin jihar kano shawarar su guji bari ana amfani da kudaden al’umma wajen yiwa wata jam’iyyar siyasa aiki musamman a zaben dake tafe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...