Maulidin gidan mahmud Adhama, ya na tunasar da mutane halayen Annabi Muhammad (S.A.W) – Mal. Ibrahim khalil

Date:

daga Abubakar zaharadden kano

Fitaccen Malamin Addinin Musuluncin nan a Najeriya kuma shugaban Majalissar Malamai ta jihar Kano Sheikh Malam Ibrahim Khaleel, ya bayyana tasirin kasancewa a tarukan Maulidi musammanma wanda ake ambato da fadan halayen Manzon ALLAH (S.A.W) kawai.

Malam Khaleel, ya bayyana hakan a wani taron Maulidin da aka gudanar a Kano wanda wani bawan ALLAH Mahmud Adahama, ke shiryawa kowacce Shekara a gidansa da ke Unguwar G.R.A.

IMG 20260704 WA0007
Talla

A cewar Malam Khaleel, shirya tarukan Maulidi irin haka yana kara tasiri wajen tunasar da mutane irin halayen Annabi Muhammad (S.A.W), musamman ma idan akayi la’akari da yadda nutsuwar taron take ruɓanya idan aka kwatanta da taron bara.

Sheikh Khaleel, ya kuma kara fito da girman ladan da wadanda ke shirya taron Maulidi irin haka za su samu a wajen ALLAH madaukakin Sarki.

Shin ko me yasa Al’ummar musulmin ke shirya tarukan Maulidi da sauran tarukan da ake ambaton ALLAH da kuma Manzon ALLAH (S.A.W) ?

Mahmud Sa’eed Adahama, shi ne wanda ya shirta taron na bana. yakuma bayyana cewa a hidimtawa Annabi muhammad (SAW) babu fashi saboda ashirye yake da ya sadaukar da duk abunda ya mallaka wajen hidimtawa annabi muhammad (SAW)

mahmuda sa’eed Adhama, yakara da cewa akowace shekara dubban jama’a daga ko ina suna dakon ranar da ze gudanar da maulidin gidansa saboda al’umma suna gamsuwa da abunda akeyi na koyarwa Annabi muhammad (SAW)

Shima a nasa bangaren da yake jawabi a gefen taron, Yariman Kano Umar Ado Bayero, ya bukaci Al’ummar jihar Kano da su rika shirya tarukan da za’a dinga fadar halayen Manzon ALLAH irin haka musamman ma idan sun samu dama.

FB IMG

Da yake jawabin godiya ga wadanda suka halarci taron, Dattijo Sa’eed Adahama, ya bayyana jin dadinsa bisa yadda Maulidin ya samu halartar dumbin mutane da dama.
dakuma Addu’ar allah yahadasu a ladan bakin daya

Za dai a iya cewa taron Maulidin wanda shine karo na 18, ya sha bam-bam da irin na shekarar Bara musamman wajen ganin nutsuwa a fuskokin mahalartan, inda daga bisani aka rufe taron da Addu’a tare da fatan samun zaman lafiya a jihar Kano dama kasa baki Daya.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

‎Tinubu ya ceci Nijeriya daga wargajewa — Kashim Shettima

‎ ‎Mataimakin shugaban Nijeriya Kashim Shettima ya ce matakan tattalin...

Da ɗumi-ɗumi: NNPC ta sanar da rage farashin man fetur a Najeriya

Kamfanin NNPC Retail ya sanar da fara bayar da...

Rikin Masarauta: ‎‘Yan Sanda Sun Jaddada Haramcin Hawan Daba da Hawan Dawakai ga Kowa a Kano

‎ ‎Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta sake jaddada cewa...

An kama mutane sama da 380 bisa zargin shaye-shaye a Kano – Gwamna Abba

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ce hukumomi sun...