Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya taya Radio Kano murnar cika shekaru 80 da kafuwa, yana mai yabawa gidan rediyon kan gudunmawar da yake bayarwa wajen wayar da kan al’umma da ci gaban jihar tsawon shekaru.
Gwamnan, wanda Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Faruk Umar Ibrahim, ya wakilta, ya bayyana hakan ne yayin bikin cika shekaru 80 da kafuwar gidan rediyon da aka gudanar a harabar Radio Kano.

Ya ce tsawon shekaru, Radio Kano ta taka muhimmiyar rawa wajen kare wa da bunƙasa al’adun Kano, wayar da kan jama’a, tare da horas da ƙwararrun ma’aikatan rediyo da suka taimaka wajen bunƙasa harkokin yaɗa labarai.
Gwamna Abba ya ce cikar Radio Kano shekaru 80 ya kamata ta zama wata dama ta ƙara bunƙasa ƙirƙire-ƙirƙire, ƙwarewa da hidima ga al’umma.
Ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafa wa Radio Kano domin ta samu damar tinkarar sauye-sauyen da ake samu a harkokin yaɗa shirye-shiryen rediyo na zamani.
Gwamnan ya kuma yi kira da a ƙara inganta kayan aikin fasaha na gidan rediyon, tare da ci gaba da horas da ma’aikata da haɓaka ƙwarewarsu, musamman ta hanyar amfani da sabbin fasahohin yaɗa shirye-shirye.
Ya buƙaci mahukunta da ma’aikatan Radio Kano da su ci gaba da riƙe ƙa’idojin aikin jarida na gaskiya da adalci, tare da amfani da kafar wajen ilimantar da jama’a, tallata ayyukan ci gaba da kuma kare al’adun jihar.
Gwamnan ya kuma yi kira ga masu aikin yada labarai da su fahimci muhimmiyar rawar da suke takawa wajen tabbatar da zaman lafiya da gudanar da zaɓuka cikin gaskiya da sahihanci, musamman yayin da ake tunkarar babban zaɓen 2027.
Ya ce ya kamata kafafen yaɗa labarai su riƙa gabatar da rahotannin da suka dace da kuma lura da yanayin da ake ciki.
Gwamna Abba ya ce: “A madadin Gwamnatin Jihar Kano, muna taya mahukunta da ma’aikatan Radio Kano murnar wannan gagarumar nasara. Muna kuma yin godiya ta musamman ga waɗanda suka yi aiki a gidan rediyon kuma yanzu ba sa cikinmu. Gudunmawar da suka bayar za ta ci gaba da kasancewa wani muhimmin ginshiƙi na tarihin Radio Kano.”
A nasa jawabin, Sarkin Rano, Ambasada Muhammad Isa Umar, ya yabawa Radio Kano bisa gagarumar gudunmawar da ta bayar wajen bunƙasa harkokin yada labarai hidimar jama’a tsawon shekaru.
Sarkin ya buƙaci ma’aikatan gidan rediyon da su ci gaba da ƙoƙarinsu wajen sanar da jama’a, ilimantar da su da kuma nishadantar da su, tare da taimakawa wajen fahimtar manufofi da shirye-shiryen gwamnati.
Tun da farko, Manajan Daraktan Radio Kano, Kwamared Abubakar Adamu Rano, ya ce cikar gidan rediyon shekaru 80 wata dama ce ta murnar gadon da ya gada, jajircewarsa wajen hidimar jama’a da kuma sauye-sauyen da yake samu domin dacewa da ci gaban fasahar zamani
Ya ce Radio Kano ta ci gaba da kasancewa muhimmiyar kafa wajen samar da ƙwararrun ma’aikatan yada shirye-shirye da kuma isar da saƙonni ga masu sauraro a faɗin Kano da sauran sassan ƙasar.
Da yake magana a madadin tsofaffin Manajojin Daraktan da suka taɓa jagorantar gidan rediyon, Alhaji Halilu Ahmad Getso, ya taya Radio Kano murnar cika shekaru 80.
Read also: Kwankwaso ya yi tsokaci game da zaben cike gurbi da akai a Kano
Read also: Dan majalisar Tarauni, Hafizu Kawu ya kaddamar da aikin titin N2.6bn a mazabar
Read also: Iftila’i: Gobara ta tashi a masarautar Kano

Alhaji Halilu Ahmad Getso, wanda ya taɓa zama Daraktan Zartarwa na Radio Nigeria Kaduna, ya yaba wa shugabancin Radio Kano na yanzu bisa shirya bikin da ya haɗa tsofaffin ma’aikatan da da na yanzu domin tunawa da tarihin gidan rediyon.
Bikin cika shekaru 80 da kafuwar Radio Kano ya samu halartar jami’an gwamnati, sarakunan gargajiya, ƙwararrun ‘yan jarida, tsofaffin ma’aikatan Gidan Radio Kano da sauran al’umma.